Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO tana sanya lafiyar mutane da rayukansu a gaban komai, a maimakon moriyar wata kasa
2020-04-30 13:39:40        cri
Le Yucheng, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a ranar 28 ga wata cewa, hukumar kiwon lafiyar kasa da kasa wato WHO tana sanya lafiyar mutane da rayukansu a gaban komai, a maimakon moriyar wata kasa.

Kwanan baya, Amurka ta sanar da dalilin da ya sa ta dakatar da biyan kudi ga WHO a matsayinta na mambar hukumar, inda ta ce, WHO ta kulla huldar kut-da-kut da kasar Sin. Dangane da lamarin, a yayin da yake zantawa da wakilin gidan rediyon kasar Amurka wato NBC, Le Yucheng ya ce, hukumar ta WHO tana sauke nauyinta yadda ya kamata, kuma tana gudanar da ayyuka bisa kwarewa. Kana ta samu amincewa da yabo daga kasashen duniya.

Mista Le ya kara da cewa, a wannan muhimmin lokacin da ake yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, kamata ya yi Amurka ta mai da hankali kan yaki da annobar, a maimakon yaki da WHO. Hakika yadda Amurka take yi ya sanya salonta ya sabawa kasashen duniya, haka kuma tana kawo cikas da barna ga kokarin da WHO take yi na gudanar da ayyukan yaki da annobar cikin hadin gwiwar kasa da kasa, da ceton rayuka, musamman ma a cikin kasashen Afirka da sauran kasashe masu tasowa. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China