Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID 19 a duniya ya kai 2549632
2020-04-24 11:28:31        cri

Alkaluman da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayar na nuna cewa, ya zuwa yanzu, yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a duniya kai kai 2549632, yawan mamata sanadiyyar cutar ya kai 175825, yayin da yawan mutanen da suka kamu da cutar a duniya a wajen kasar Sin ya haura miliyan 2.46.

Ban da wannan kuma, WHO ta kira wani taron ministoci a jiya Alhamis, inda ministan kiwon lafiya na kasar Afrika ta kudu ya sanarwa duniya halin da kasar ke ciki, da manufar da kasar ke dauka na kebance duk jama'a cikin gida ba tare da bata lokaci ba, wanda ya samu amincewa daga kasashen duniya. Ban da wannnan kuma, Afrika ta kudu ta jaddada cewa, jagorancin da WHO ta baiwa kasar da ma duk duniya na da muhimmanci matuka. Kana kuma, kasar tana goyon baya da kuma amincewa da jagorancin Tedros Adhanom Ghebreyesus a hukumar WHO. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China