Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO za ta ci gaba da hada kai da kasashen duniya domin rage gibin da ke tsakaninsu a fannin yaki da annobar COVID-19
2020-04-23 12:33:16        cri

Jiya Laraba Tedros Adhanom Ghebreyesus, babban sakataren hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ya ce, za mu dade muna fama da annobar cutar numfashi ta COVID-19. Don haka da sauran rina a kaba.

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi nuni da cewa, kawo yanzu hukumar ta samu rahotanni kusan mutane miliyan 2 da dubu 500 sun kamu da cutar. Yanayin yaduwar cutar a yankunan duniya sun sha banban. Duniya ba za ta koma kuma ba za ta taba komawa yadda ta ke a da ba. Ya zama tilas mu samar da duniya mai koshin lafiya, da kwanciyar hankali, wadda kuma za ta kara shirya tinkarar abubuwa na ba-zata.

Dangane da zargin da aka yi wa WHO wai ya kamata ta yi gargadi a kan lokaci, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi bayyyana cewa, hukumar ta WHO ta yi gargadi a kan lokaci tun kusan watanni 3 da suka gabata. A wancan lokaci, mutane 82 ne kawai suka kamu da cutar COVID-19 a duniya, baya ga kasar Sin. Kasashen duniya na da isasshen lokacin da za su shirya matakan kandagarki da dakile yaduwar annobar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China