Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta taya Wuhan murnar ganin bayan cutar COVID-19
2020-05-02 16:38:46        cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi maraba da labarin dake cewa, babu wani mai dauke da cutar COVID-19 dake kwance a asibitin birnin Wuhan na kasar Sin, inda ta jinjinawa namijin kokarin da kasar ta yi wajen dakile annobar.

Bayan shafe sama da watanni 3 ana yaki da cutar, yanzu a birnin Wuhan dake yankin tsakiyar kasar Sin, da ya taba kasancewa inda cutar COVID-19 ta fi kamari, an sallami dukkan wadanda suka kamu da cutar COVID-19 dake kwance a asibiti, bayan sun warke, a ranar Lahadin da ta gabata.

Yayin wani taro ta kafar bidiyo, shugabar shirin ayyukan lafiya na gaggawa na WHO, Maria Van Kerkhove, ta ce abun farin ciki ne jin cewa babu wani dake cikin yanayi mai tsanani ko yake dauke da cutar a birnin Wuhan.

Maria Kerkhove, wadda ke cikin tawagar kwararru na hadin gwiwa tsakanin Sin da WHO da suka ziyarci kasar Sin a watan Fabreru domin nazartar yanayin da ake ciki, ta ce kasar Sin ta yi namijin kokari wajen dakile yaduwar cutar.

Ban da wannan kuma, yayin wani taron manema labarai da aka yi a wannan rana, jami'in hukuma mai kula da haliln ko ta kwana Michael Ryan ya ce, akwai dimbin shaidu da masu nazarin kimiyya da dama suka samu sun tabbatar cewa, wannan cuta na samun asali daga indallahi, kazalika darakta janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya mai da martani dangane da zargin da aka yi wa hukumar na gazawa wajen ayyana cutar COVID 19 a matsayin matsalar kiwon lafiya dake bukatar daukin gaggawa daga kasa da kasa a kan lokaci, inda ya ce, WHO ta yi gargadi kan lokaci, matakin da ya baiwa duk duniya isashen lokacin tinkarar cutar. Ya ce a ranar 30 ga watan Jarairu, kwamitin hukumar ya cimma matsayar sanar da cutar a matsayin matsalar lafiya dake bukatar daukin gaggawa, kuma a waccan lokaci mutane 82 ne kadai suka kamu da ita a duniya, ban da a kasar Sin, kuma babu wanda ya rasa ransa sakamakon cutar, abin da ya bayyana cewa, akwai isashen lokacin yin kandagarkin cutar.
Alkaluman da WHO ta gabatar na nuna cewa, kawo yanzu yawan mutanen da suka kamu da cutar a duniya ya kai 3,181,642, adadin da ya haura miliyan 3 da dubu 90, tare da yawan mamata ya kai 224,301, ban da kasar Sin.(Fa'iza Mustapha, Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China