Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar lafiyar kasar Sin ta samu rahoton sabbin mutane 1886 da suka kamu da cutar COVID-19
2020-02-18 11:28:15        cri
Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta samu rahoton sabbin mutane 1886, wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin babban yankin kasar a jiya Litinin, kana kuma, akwai sabbin majinyata 1097 wadanda ke cikin matsanancin hali, kana an kara samun mutum 98 wadanda suka rasu sakamakon cutar, yayin da aka kara samun mutane 1432 wadanda aka zargi da kamuwa da cutar. Haka kuma a jiya Litinin, an kara samun mutane 1701, wadanda aka sallame su daga asibiti, bayan da suka warke daga cutar, kuma mutane 27908 masu alaka sosai da wadanda ke dauke da cutar, an soke sa ido a kansu.

Zuwa karshen jiya Litinin, a duk fadin kasar Sin, gaba daya akwai mutane 12552 wadanda aka sallama daga asibiti bayan da suka warke daga cutar numfashi ta COVID-19, kuma jimillar mamatan ta kai 1868, yayin da kuma aka tabbatar da mutane 72,436 wadanda suka kamu da cutar. Har ma akwai mutum 6242 a duk fadin kasar da ake zargi sun kamu da cutar.

A lardin Hubei ma, wato inda cutar nan ta fi kamari, kawo yanzu akwai mutane 50338 da aka tabbatar sun kamu da cutar, ciki har da 10970 wadanda ke cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai. Sa'annan adadin wadanda suka warke daga cutar ya kai 7862, yayin da mutum 1789 suka rasa rayukansu, ciki har da wasu 1381 a Wuhan, babban birnin lardin. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China