![]() |
|
2020-02-17 14:09:48 cri |
A wannan karo dai, duk mambobin rukunin jinya sun sami tikiti na musamman. A kan wannan tikiti an rubuta cewa, yau ne lokacin tafiya, ranar dawowa kuma ita ce lokacin da aka samu nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19, matakin da ya bayyana nauyin dake wuyan rundunar sojojin kasar Sin, wato idan jama'a na da bukata, za su kai duk inda ake bukatar tallafi, da kuma niyyarsu ta samun nasara.
Ban da wannan kuma, an rubuta sunan kowane hafsa mai aikin jinya a kan tikiti da lakabinsu wato "VIP--soja mai aikin jinya", don nuna girmamawa ga dakarun. (Amina Xu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China