2020-02-17 13:13:12 cri |
A jiyan dai, jimillar yawan mutanen dake dauke da cutar ya kai 57,934, daga cikinsu 10,644 na cikin hali mai tsanani, kuma wadanda suka warke daga wannan cuta ya kai 10,844. Kaza lika yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar ya kai 1,770 a jiyan, yayin da yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 70,548, kuma wadanda ake zaton sun kamu da ita ya kai 7,264. Ban da wannan kuma, mutane dake da alaka da wadanda suka kamuwa da cutar da aka gano ya kai 546,016, daga cikinsu wadanda ake sa ido kansu ya kai 150,539.
Dadin dadawa, akwai kuma karin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a lardin Hebei da yawansu ya kai 1933, daga cikinsu 1690 na zaune a birnin Wuhan, kana karin mutanen da suka warke ya kai 1,016, daga cikinsu 543 a birnin Wuhan. Har wa yau, akwai karin mutane 100 da suka mutu, daga cikinsu 76 a birnin Wuhan. Ban da wannan kuma, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 49,847. 36,385 daga cikinsu na daga Wuhan. Daga cikinsu wadanda suke fama da mawuyacin yanayi ya kai 9,797, daga cikinsu 8,056 na cikin Wuhan.
Akwai kuma mutanen da suka warke daga cutar da yawansu ya kai 6,639, daga cikinsu 3,458 na daga Wuhan, kana yawan mutanen da suka rasu ya kai 1,696, daga cikinsu Wuhan na da 1309. Sannan kuma, wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 58,182, 41,152 na cikin Wuhan. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China