2020-02-17 12:26:24 cri |
Bisa sabon salon yaki da ake yi da wannan annoba, duk wanda aka yi wa gwaji bisa alamun cutar numfashi na "CT scan" bisa alamu da suka bayyana, ana sanya shi cikin wancan rukuni, kamar dai yadda hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar da daukar wannan mataki.
A ranar Laraba, a cewar hukumar lafiyar lardin Hubei, an samu sabbin mutane 14,840 da suka kamu da cutar, ciki hadda mutum 13,332 da aka yi wa cikakken gwaji, adadin da ya kasance mafi yawa da aka samu a rana guda, tun bayan bullar cutar. Ana kuma sa ran yin hakan, zai baiwa wadanda suka kamu da cutar damar samun kulawar gaggawa.
Da take tsokaci kan hakan, babbar jami'ar sashin aikin jinya na asibitin Jinyintan na birnin Wuhan madam Wu Jing ta ce gano masu dauke da cutar, da fara yi musu magani cikin sauri, na daga muhimman matakai na dakile yaduwar cutar ta COVID-19.
Shi ma wani kwararre da ke jagorantar tawagar jami'an lafiyar Shanghai dake ba da tallafi a Hubei Chen Erzhen, ya ce a kan samu wadanda aka yi wa gwajin farko har karo 4 a jere, kafin daga karshe a tabbatar da suna dauke da wannan cuta, wanda hakan ke nuni ga yiwuwar samun kuskure a gwaje-gwajen farko, don haka yi wa wadanda ake tunanin suna dauke da cutar karin gwaji, na daga muhimman dabarun tabbatar da masu dauke da ita. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China