Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta alkawarta kara azama wajen samar da kayan bukata ga Wuhan
2020-02-18 10:20:36        cri

Mahukuntan kasar Sin sun sha alwashin yin aiki tukuru, wajen tabbatar da wadatar kayayyakin bukatu na yau da kullum a birnin Wuhan da kewaye, inda cutar numfashi ta COVID-19 ta fi kamari, ta hanyar inganta hadin gwiwa tsakanin lardunan kasar.

Wata takardar bayani da ma'aikatar cinikayyar kasar ta fitar a jiya Litinin, ta ce za a kara azamar samarwa birnin da yankunan dake kewayen sa kayayyakin masarufi da na abinci, kamar ganyaye, da nama, da shinkafa da man girki, musamman a wannan gaba mai muhimmanci ta kara rufe lardin Hubei, domin dakile yaduwar cutar.

Takardar ta ce a yanzu haka, aikin kandagarki da shawo kan annobar yana cikin wani mataki mai tsanani, don haka ya zama wajibi dukkanin sassan masu ruwa da tsaki su tabbatar da nasarar shigar kayan masarufi wannan yanki, domin kaucewa yankewar kayan a kasuwa.

Har ila yau, takardar ta ce akwai bukatar daidaita yanayin komawa aiki ga kamfanonin cinikayya da kasuwanci, da masu ayyukan ba da hidima, ta yadda komai zai gudana bisa tsari. Ana fatan kananan hukumomi za su daidaita matsaya, tsakanin aikin dakile yaduwar cutar ta COVID-19 da kuma shirin kamfanoni na komawa bakin aiki.

Bugu da kari, takardar ta ce ya wajaba, yankunan da aka riga aka shawo kan yaduwar cutar, su kasance cikin shirin taimakawa sassan da ke fama da ita, ta hanyar fadada samar da hajoji da fitar da su domin amfanin masu bukata a kan lokaci. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China