Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan sabbin masu kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 na raguwa cikin kwanaki 13 a jere a wajen lardin Hubei
2020-02-17 12:03:04        cri
Rahotanni na cewa, yawan sabbin masu kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19, a wajen lardin Hubei na ta raguwa cikin kwanaki 13 a jere, tun daga ranar 3 ga watan nan. Hukumar lafiyar kasar Sin ta ce an samu karin mutum 115 wadanda suka kamu da cutar a wajen Hubei a jiya Lahadi. Alkaluman hukumar sun nuna cewa, a wajen lardin na Hubei, an samu sabbin wadanda suka kamu da cutar 890 a ranar 3 ga watan kadai.

Kaza lika a jiya Lahadi, hukumar ta samu rahoton jimillar karin mutane 2,048, da suka kamu da cutar a lardunan kasar 31, da yankin aikin soji na Xinjiang, ciki hadda mutane 1,933 a lardin Hubei. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China