Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lardin Hubei ya fitar da karin matakai na yaki da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19
2020-02-17 10:19:23        cri
A jiya Lahadi, mahukunta a lardin Hubei na kasar Sin inda cutar numfashi ta COVID-19 ta fi kamari, suka sanar da karin matakan zurfafa yaki da cutar da ake aiwatarwa a lardin, a wani mataki na tabbatar da nasarar shawo kan ta baki daya.

Matakan dai sun hada da takaita zirga-zirgar ababen hawa a daukacin lardin, ga duk ababen hawan da ba ayyukan gaggawa suke gudanarwa ba, tare da rufe duk wasu wuraren taruwar jama'a da ba su zama dole a bude su ba.

A cewar takardar umarni da gwamnatin lardin ta fitar, za a aiwatar da wadannan matakai ne, kasancewar an shiga wani mataki mai muhimmanci na yaki da yaduwar cutar, inda ake fuskantar yanayi mai tsanani.

Takardar ta kuma ce, za a ci gaba da karfafa tsarin tantance lafiyar mutane, ta yadda za a san matsayin kowa. Kaza lika an umarci jama'a da cewa, da zarar an samu wanda ya nuna alamun zazzabi ko tari, a gaggauta sanar da mahukuntan unguwa ko kauye.

Ya zuwa daren ranar Asabar, lardin Hubei ya tabbatar da cewa, jimillar wadanda wannan cuta ta COVID-19 ta harba sun kai mutum 56,249, ciki hadda mutum 39,447 dake kwance a asibitoci, da kuma wasu 8,439 dake ciki matsanancin halin rashin lafiya, baya ga mutum 1,957 dake halin mutu kokwai rai kokwai. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China