Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Nijeriya ya amince da murabus din tsohon alkalin alkalan kasar
2019-06-11 10:20:39        cri

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya amince da murabus din da tsohon alkalin alkalan kasar Walter Onnoghen, wanda aka tuhuma da laifin bayyana kadarorin da ya mallaka, ya yi bisa radin kansa.

A cewar Muhammadu Buhari, murabus din na Walter Onnoghen ya fara aiki ne daga ranar 28 ga watan Mayu, watanni 4 bayan ya dakatar da shi daga aiki a ranar 25 ga watan Janairu.

An dakatar da tsohon alkalin alkalan ne saboda ya take dokar da'ar ma'aikata, bayan an tuhume shi da mallakar wasu asusun banki dake dauke da miliyoyin daloli da bai bayyana ba.

A ranar 23 ga watan Fabrairu ne kotun da'ar ma'aikata ta kasar ta ba jami'an tsaro umarnin kama Onnoghen, gabanin zaman shari'ar da ta yi, inda jami'an tsaron suka killace ofishinsa.

An fara yi wa Onnoghen shari'a ne bayan korafin da wata kungiyar kare hakkin al'umma ta shigar gaban kotun, tana mai zarginsa da mallakar wasu asusun banki da yake ajiyar tsabar kudin cikinsu da kansa.

An yi zargin ana tafiyar da asusun na sirri ne a wani yanayi da ya sabawa dokar da'ar ma'aikata ta kasar da kuma sahihiyar hanyar hada-hadar kudi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China