Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya: An baza jami'an kiyaye hadurra domin kiyaye lafiyar matafiya yayin bukukuwan sallah
2019-06-01 15:20:56        cri
Hukumar kiyaye hadurra a Tarayyar Najeriya FRSC, ta ce ta baza jami'an ta da yawan su ya kai a kalla 36,000 sassan kasar daban daban, domin gudanar da sintiri da kiyaye dokoki, gabanin bukukuwan karamar sallah da za a shiga nan da 'yan kwanaki.

Kakakin hukumar reshen jihar Lagos Bisi Kazeem, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafinta, inda ya ce matakan da aka dauka, sun yi daidai da manufar hukumar, na gudanar da sintirin musamman yayin bukukuwa, da nufin rage cunkoso, da hadurran ababen hawa ko rasa rayuka.

Kazeem ya kara da cewa, burin su shi ne tabbatar da an gudanar da bukukuwan karamar sallah lami lafiya, cikin tsaro da zirga zirgar mutane da ababen hawa yadda ya kamata a daukacin sassan kasar.

Jami'in ya kuma yi kira ga masu ababen hawa, da su baiwa jami'an hukumar ta FRSC da sauran jami'an tsaro hadin kai, ta yadda za su gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China