Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Nijeriya za ta wallafa nazarinta kan cin hanci a watan Satumban bana
2019-06-11 09:41:11        cri

Gwamnatin Nijeriya ta ce, za ta wallafa sakamakon nazarin da ake yi kan cin hanci a kasar a watan Satumban bana.

Daraktan aikin na hukumar kididdiga ta kasar, Isiaka Olarewaju ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, babban birnin kasar.

Aikin shi ne nazarin jama'a na biyu da aka yi a kasar kan inganci da sahihancin aikin gwamnati a bana.

Manufar aikin ita ce, tattaro bayanai da za su kasance shaida kan nau'ikan cin hanci dake tasiri kan rayuwar yau da kullum na 'yan kasar, da gano yanayin bazuwarsa da nau'in da ya fi bazuwa.

Daraktan ya ce, an tura ma'aikata masu tattaro bayanai, kuma za a kammala nazarin zuwa karshen watan nan na Yuni.

Ya kara da cewa, shugaban masu kididdiga na hukumar, zai bayyana sakamakon nazarin ga al'umma kafin ko a cikin watan Satumba. Yana mai cewa, an tura jami'ai 20 zuwa ko wace jiha ta kasar.

Isiaka Olarewaju, ya ce nazarin zai ba gwamnatin da 'yan kasar damar nazarin matakin ci gaban da aka samu cikin shekaru 2 da suka gabata, la'akari da matsayar gwamnatin kasar na yaki da cin hanci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China