Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tijjani Muhammad-Bande ya zama sabon shugaban babban zauren MDD karo na 74
2019-06-05 10:07:19        cri
Babban Zauren MDD karo na 73 ya zabi wakilin dindindin na Nijeriya dake majalisar, Mista Tijjani Muhammad-Bande a matsayin sabon shugabansa a sabon zagaye a jiya Talata, inda zai yi rantsuwar kama aiki a watan Satumban bana.

A jawabin da ya gabatar bayan ya ci zabe, Tijjani Muhammad-Bande ya ce zai ba da muhimmanci sosai ga batun tabbatar da zaman lafiyar da karko, da kawar da talauci, da kara daukar matakan tinkarar sauyin yanayi da ingiza samun bunkasuwa a dukkanin fannoni da sauransu.

Babban sakataren MDD Mista António Guterres ya ce, Tijjani Muhammad-Bande na da wayewar kai kan kalubalen da nahiyar Afrika ke fuskanta a halin yanzu. Ya kara da cewa, sabon shugaban zai fuskanci dimbin ayyuka, musamman la'akari da jerin muhimman tarurukan da za a kira a watan Satumba mai zuwa, yana fatan Muhammad-Bande zai yi shiri tsaf a watanni masu zuwa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China