2019-06-04 09:27:13 cri |
Kakakin rundunar kawancen ta MNJTF, Timothy Antiga, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, an kashe 'yan ta'addan ne yayin samamen da aka kai yankunan Arege da Malkonory da kuma Tumbum Rego.
Ya ce aikin wani bangare ne na matakin soji da aka dauka domin fatattakar mayakan IS daga yankin tafkin Chadi.
Sai dai, ya ce jami'an rundunar 4 sun samu rauni yayin bata kashin da aka yi tsakaninsu da 'yan ta'addan, kuma tuni aka garzaya da su asibiti don samun kulawa.
Jami'in ya ce rundunar ta kuduri niyyar cimma burinta, yana mai kira ga mutanen yankin su ci gaba da ba su goyon baya.
A watan Fabrerun bana ne rundunar kawance ta MNJTF, ta kaddamar da sabon aikin fatattakar mayakan Boko Haram daga yankin tafkin Chadi. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China