Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Borno na bukatar malamai 6000 bayan fuskantar ta'addancin mayakan Boko Haram
2019-06-10 10:15:20        cri

Hukumomi a tarayyar Najeriya sun ce kimanin karin malaman makaranta dubu 6,000 ake bukata domin samar da ingantaccen ilmi a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

"Gwamnatin tana gina makarantu inda ake samar da kyakkyawan muhallin koyon karatu, sai dai kuma malamanmu ba su da kwarin gwiwa," Jibril Muhammed, shugaban kungiyar malaman makarantu ta Najeriya wato (NUT) shi ne ya bayyana hakan a Maiduguri, babban birnin jihar. "Na yi amana cewa idan an samu dukkan hanyoyin da za'a kara wa malamanmu kwarin gwiwa, to matsalolin dake damun fannin ilminmu za'a magance su."

Ya bayyana hakan ne bayan kammala aikin rukunin manyan makarantu 40 wadanda gwamnatin ta giggina domin daukar nauyin karatun yara 53,000 wadanda mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram suka mayar da su marayu a jihar.

Muhammed ya yaba wa gwamnatin sakamakon yadda ta baiwa bangaren ilmi fifiko a jihar, sai dai ya ce akwai bukatar a kara ba da fifiko wajen kyautata jin dadin rayuwar malaman makarantun.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China