Masu nazari da suka fito daga kasar Australia sun kaddamar da sakamakon nazarinsu a kwanan baya, inda suka yi nuni da cewa, zauna kan kujera cikin dogon lokacin yayin da ake aiki zai kara barazanar kamuwa da ciwon sankara a hanji. Masu nazarin sun ba da shawarar cewa, kamata ya yi mutane su kara motsa jiki, a kokarin rage irin wannan barazana.
Masu nazarin daga hadaddiyar kungiyar nazarin ciwon sankara ta Victoria ta kasar Australia sun yi karin bayani da cewa, nazarin da suka gudanar ya shaida cewa, idan mutane sun dade suna zauna kan kujera yayin da suke aiki, sai barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da ciwon sankara a hanji za ta karu da kaso 44 cikin dari. Amma idan sun yi tafiya da kafa ko kuma hawan keke zuwa aiki da kuma komawa gida, ko kuma motsa jiki ta hanyar da ta dace a ofis, sai barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da ciwon sankara a uwar hanji za ta ragu.
Masu nazarin sun ci gaba da cewa, nauyin jiki, shan taba, yawan giyar da ake sha, su ne manyan hadarrukan kamuwa da ciwon sankara, zauna kan kujera cikin dogon lokaci shi ma yana kawo illa ga lafiyar dan Adam. Hakika dai, idan mutane sun dade suna zauna kan kujera, sai barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da ciwon sankara a uwar jiki ta fi wadanda su kan motsa jiki kullum yawa. Amma duk da haka zauna kan kujera cikin dogon lokaci, ba wani munanan dalilin da ya haifar da kamuwa da ciwon sankara ba. Kowa ya sane da cewa, shan taba, shi ne babban hadarin kamuwa da ciwon sankara a huhu, amma zauna kan kejera cikin dogon lokaci bai kai munin haka ba.
Masu nazarin na kasar Australia da suka gudanar da nazarin sun yi nuni da cewa, a baya, ba mu lura da cewa, zauna kan kujera cikin dogon lokaci yayin da ake aiki zai haifa da kamuwa da ciwon sankara a hanji ba. Idan mutane sun je aiki da kuma komawa gida ta hanyar motsa jiki, kamar yin tafiya da kafa, hawan keke da dai sauransu, sai za a taimaka wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sankara a hanji. Sabili da haka ne kamata ya yi kamfanoni su karfafa gwiwar ma'aikatansu su dan motsa jiki a kai a kai, kana kuma su kebe wuraren ajiye kekune da sauran manyan ababen da suka taimaka wajen zuwa aiki da komawa gida ta hanyar motsa jiki.
Dangane da alakar da ke tsakanin yin zaman rayuwa ta hanyar da ta dace da kuma kamuwa da ciwon sankara, Zhang Chunji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta gaya mana cewa, za a iya yin rigakafin kamuwa da ciwon sankara da yawansu ya kai kasha 1 cikin kasha 3 ne ta hanyar yin zaman rayuwa ta hanyar da ta dace, alal misali, motsa jiki da cin abinci yadda ya kamata, kaucewa shan taba, da rage shan giya. (Tasallah Yuan)