Masu karatu, yanzu haka kasashen duniya na yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, ciki had da kasar Sin da kasar Nijeriya, amma kar mu manta da wata mummunar annoba ta daban a kasar wato zazzabin Lassa da ake fama da ita a wasu sassan Nijeriya.
Kwanan baya, rahotanni daga kamfanin dillancin labaru na Nijeriya(NAN) sun ruwaito mana cewa, darektan Cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Nijeriya wato NCDC a takaice mista Chikwe Ihekweazu ya yi nuni da cewa, cibiyarsa ta tsara matakan yaki da annobar cutar zazzabin Lassa a sassa daban daban na kasar, a kokarin dakile yaduwar annobar.
Annobar cutar zazzabin Lassa, wani nau'in mummunar annoba ce da take iya yaduwa tsakanin mutane sakamakon kwayar cutar Lassa. Masana lafiya sun yi amanna cewa, beraye da dangoginsu ne ke yada annobar. Wannan annoba mai hadari ta Yadu a kasashen Nijeriya, Saliyo da wasu kasashen yammacin duniya. Ana kiran annobar da sunan "zazzabin Lassa"ne saboda garin Lassa da ke arewa maso gabashin kasar ta Nijeriya, inda aka samu mutum na farko da ya kamu da annobar a shekarar 1969.
Masu karatu, ya zuwa yanzu dai babu allurar rigakafin annobar cutar zazzabin Lassa a duniya. To, ta yaya za mu iya kare kanmu daga annobar? Yau mun gayyaci Zhang Chuji, wata likita dake aiki a asibitin Tiantan na Beijing inda ta gaya mana yadda za a iya yin kandagarkin annobar. Inda ta ce, killace ko kebe wadanda suka kamu da cutar akan lokaci yana da matukar muhimmanci. Sa'an nan ya zama tilas iyalan wadanda suka kamu da cutar da kuma ma'aikatan lafiya su guji taba jini, fitsari, kasha ko najasa, da ruwan da ke fita daga jikinsu. Haka kuma dole ne a tsabtace muhalli sosai, tare da karfafa matakan kashe beraye. Sai dai kuma, bai dace a taba beraye da kuma fitsarinsu da kashinsu kai tsaye ba. Har ila yau kuma a adana abinci a robar da iska ba ta shiga.
Yawancin wadanda annobar ta harba ba sa nuna wasu alamu. Idan annobar ta tsananta, masu wadanda suka kamu da annobar su kan ji zazzabi, rashin karfin jiki, ciwon kai, amai da ciwon gabobi. Wasu kuma jini kan zuba ta baki ko ciki da ma hanjinsu. Daga cikin wadanda suka tsira daga annobar, kashi 1 cikin kashi 4 su kan zama bebaye.
Idan an kamu da annobar ta zazzabin Lassa, ya kamata a gaggauta zuwa asibiti domin ganin likita don samun magani. Zhang Chuji ta kara da cewa, likitoci kan bai wa wadanda suka kamu da annobar maganin Ribavirin don yaki da kwayoyin cutar. Haka kuma akwai bukatar kara shan maganin da wuri, yin haka zai kara yin aiki yadda yadda ya kamata. Kana kuma likitoci kan dauki matakan tabbatar da isasshen ruwa a cikin jikin masu kamu da cutar da kuma taimaka musu jin dadi.
Chikwe Ihekweazu ya nuna cewa, cibiyar ta NCDC za ta sanar da barazanar annobar zazzabin Lassa ta gidan rediyo, gidan talebijin, jaridu, da shafukan sada zumunta kamar Facebook da Twitter, tare da hada kai da unguwanni wajen daukar matakan yaki da wannan cuta.
Jami'in ya kara da cewa, cibiyar NCDC ta inganta karfinta na tabbatar da ko an kamu da annobar ta zazzabin Lassa ko a'a.