Taron kasashe mawadata na duniya(taron kasashen G20) wanda za a fara a birnin Hangzhou na kasar Sin yana jan hankalina kana taron ya zo a dadai lokacin da kasashen duniya ke fuskantar matsalar koma-bayan tattalin arziki masamman ma kasashenmu na Afirka masu tasowa. Muna fata taron na birnin Hangzhou zai bada muhimminci ga lalibo hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalar tattalin arziki duniya.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.