South China Sea
Yakamata kotun duniya dake birnin Hague su yi dogon tunani da hangen nesa kafin su yanke hukuncin karshe da kasar Philiphines suka nemi kotun su yi, bisa takaddamar ikon mallakar tekun kudancin kasar Sin(south China Sea) wanda ke daukan hankalin kasa da kasa a halin yanzu da lamura ke kara dagulewa tsakanin kasashen China da Philiphines. Kana ina kira ga kasar Amurka da kawayenta yammacin turai da su daina tsoma baki da katsa-landan da yin shishshigi a siyasar dake sake daukan sabbin salo adangane da halin da ake ciki a tekun kudancin kasar Sin tsakanin kasar Sin da kasar Philiphines. Darewa teburin yin sulhu dan tattauna batun halin da ake ciki a tekun kudancin kasar Sin, zai fi zama alfanu sosai ga makomar kasashen 2, kana kasashen China da Philiphines da Vietnam sune ya dace su magance matsalar da ta kunno kai a tekun kudancin kasar Sin. Kana ina kira ga Kasar Amurka da kawayenta yammacin turai da su kawo karshen ingizan da suke yi a yankin tekun kudancin kasar Sin, domun ci gaba da yin ingizo da Amurka ke yi, ka iya kara dagula lamuran da ake ciki a tekun kudancin kasar Sin. Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku