in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ra'ayina game da Shirinku na Hausawa a kasar Sin
2016-04-18 09:42:00 cri
Zuwa ga Malama Fatima Liu CRI Hausa,

Bayan gaisuwa mai tarin Yawa dafatan kunanan lafiya.

Bayan haka dalilin rubuto muku wannan sako shine naji dadin shirin da kuka gabatar a yau na Allah daya gari banban wanda M. Lubabatu ta gabatar wanda kuka tattauna da wasu dalibai Hausawa da suke karatu a kasar Sin kuma wanda a shiri nagaba zaku tattauna da 'yan kasuwa. To tun danaga sakon wannan shiri a shafinku na zumunta na facebook na Hausawa a kasar Sin naji dadi sannan nasan tabbas wannan shiri zai kuma jawo hankalin Hausawa dun inda suke a fadin duniya domin daya daga cikin al'adar Hausawa shine fatauci wato tafiye-tafiye domin zan Iya tunawa tun ina yaro nasan iyaye suna tafiye domin ance tafiya mabudin ilima kuma kasar tabbas wani gurine mai mahimmamci a duniya kuma na samun ilimi, domin jin hirar da kukayi da dalibai masuyin degree na daya ko na biyu a fannin kimiyya na lantarki da injiniyarin dadai sauransu, sai na tuna tun muna yaro mun koya a makarantar Islamiyya cewa Manzon Allah Annabi Muhammadu S.A.W yace 'Ku nemi ilimi koda a kasar Sin' kaga wannan magana ta fiyayyen Halitta ta kuma tabbatar da mahimmamcin kasar Sin a tarihin duniya musammam a gurin al'ummar Hausawa. A karshe inafan za'aci gaba da gabatar da shirye masu mahimmamci irin wannan. Domin wannan shiri yakuma samun son da sha'awar kawo ziyara ta gani da ido a kasar Sin.

Ina muku fatan alheri.

Wassalam, Abdulkadir Ibrahim, G.C.L.C Kano, Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China