'Yan kasuwa, asalin 'yan Najeriya, kamar su Muhammad Mustapha Abba da Muhammad Bello da Rahma Adamu Abdullahi sune aka nuna da kawo labaran su game da irin kasuwancin da suke yi a kasar Sin. Kowanen su ya bayyana lokacin da ya fara zuwa kasar Sin da kuma irin kasuwancin da yake yi a kasar Sin din. Abin akwai ban sha'awa ainun.
Haka kuma, kowannensu ya bayyana burinsa da hangen nesan sa bias ga yanayin cinikayya day a kan gudanar, da kuma bayyana yanayin riba ko moriyar da su kan samu.
Hakika, wannan shiri ya nuna irin yadda ake samun bunkasuwa mai nagarta a sanadiyyar cinikayya tsakanin Sinawa da Hausawa wadanda ke yin aiki tukuru domin ci gaba. Na yi na'am da wannan shiri, ina kuma fata zaku kara fadada shirin ta yadda zai kun shi wasu bangarori na rayuwar 'yan Najeriya dake kasar Sin. Hakika, kun cancanci yabo da kuka gabatar da wannan shiri a wannan lokaci.
Naku,
Salisu Muhammad Dawanau