Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri ga ma'aikatanku baki daya, da fatan duk kuna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, ina farin cikin sanar da ku cewa, yau 20 ga watan Satumba na samu zarafin sauraron maimaicin shirinku na 'Sin da Afirka' ta shafin ku na yanar gizo.
Ko shakka babu, naji dadin sauraron wannan shiri sakamakon hira da malama Suwaiba ta yi da karamin ministan harkokin wutar lantarki na Nijeriya malam Muhammad Wakil kan ziyararsu a kasar ta Sin tare da kulla yarjejeniya tsakanin kasashen biyu don bunkasa sha'anin wutar lantarki dake fuskantar matukar koma baya a kasar ta Nijeriya.
Hakika, na yi matukar farin ciki dangane da yarjejeniyar da kasata Nijeriya ta kulla da kasar Sin kan harkar wutar lantarki, musamman yadda kasar ta Sin ta amince da bayar da tallafin makudan kudi har dala biliyan 4, yayin da ita Nijeriya za ta bayar da dala biliyan daya. Wannan ci gaban ya karfafa min gwiwa bisa la'akari da yadda kasar Sin ke son yin amfani da karfin tattalin arziki da fusaharta wajen taimaka wa kasar ta Nijeriya fita daga matsalar karancin wutar lantarki da ya riga ya dabaibaye ta kuma ta kasa shawo kan matsalar.
Binciken da aka gudanar a baya bayan nan, ya nuna cewa fiye da kashi 57% na 'yan Nijeriya ba sa samun hasken wutar lantarki da suke bukata a yau da kullum ba, lamarin da ke dada haska irin tsanantar da halin rashin hasken lantarki ke ciki a kasar.
Dangane da haka, ina fatan wannan yarjejeniya ta samar da wutar lantarki za ta kai ga cimma nasara domin kasar ta Nijeriya ta samu sukunin farfado da sha'anin samar da hasken lantarki wanda kasar ke matukar bukata wajen bunkasa bangaren masana'antu da sauran harkokin tattalin arziki.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria