Matakan tsaftace hannu
A rika wanke hannu akai-akai
o A wanke hannu bayan da aka je bayan gida.
o A wanke hannu bayan da aka canja auduga.
o A wanke hannu bayan da aka yi atishawa, tari, ko fyace hanci.
o A wanke hannu kafin da kuma bayan da aka dafa abinci.
o A wanke hannu bayan da aka taba kwai ko naman da ba a dafa ba.
o A wanke hannu bayan da aka kwashe datti ko shara.
o A wanke hannu bayan da aka taba dabobi ko najasansu.
o A wanke hannu bayan da aka taba kudi, saboda yadda jama'a ke mu'amula da kudade a kowane lokaci.
o A wanke hannu bayan da aka taba jini.