140815-wanke-hannu.mp4
|
Idan kana wanke hannunka a kai a kai, hakan zai taimake ka da ma wadanda ke kusa da kai kasancewa cikin koshin lafiya tare da hana yada kwayoyin da ke haddasa cututtuka irin su bacteria da Viruses, sannan zai kawar da kazantar da ke hannun. Ko da kana wanke hannunka, kamata ya yi ka wanke su yadda ya kamata kuma a kai a kai.
Wanke hannu
1. Jika hannu: Ka wanke hannunka da ruwa mai dumi domin ba kamar yadda wasu ke cewa ba, wai ruwan zafi ba ya fitar da kwayoyin cuta yadda ya kamata kamar ruwan dumi, sannan zai iya yin illa ga fatar hannu idan ya hadu da kumfan wasu sabulai.
2. Amfani da sabulu: Amfani da kowa ne irin sabulu zai tamaka wajen tsaftace hannu, amma idan har amfani da kowa ne irin nau'i na sabulu ko kalansa, ko kamshinsa zai taimaka wa mutum ya rika wanke hannunsa akai-akai, to kana iya yin hakan, sai dai sabulun yau da kullum ya fi ruwan sabulu na zamani.
3. Hada kumfa: Yana da kyau mutum ya cuda hannayensa gaba da baya tsakanin yatsu har zuwa wuyan hannu a lokacin da mutum yake wanke hannunsa, sannan kada a manta a wanke ciki da wajen faratu.
4. A wanke hannu na tsawon kimanin dakikoki 20-30: Wannan shi ne lokacin da ya kamata a ce mutum ya dauka a lokacin da yake wanke hannunsa, sannan a tabbatar da cewa an cuda hannu ta yadda kumfan zai ratsa ko'ina a hannun.
5. Wanke hannu sosai: Bayan an cuda hannun yadda ya kamata, sai kuma a sanya su a karkashin ruwan da ke kwarara daga famfo yatsu na kallon kasa ba tare da an taba daron wanke hannun ba ta yadda dukkan kumfan da ke jikin hannun zai wanku sarai, wannan mataki zai wanke duk wata kwayar cuta da kuma sabulun da ke jikin hannun.
6. Ka yi amfani da tawul wajen rufe famfon ruwa, musamman a bayan gidan da jama'a ke amfani da shi: Amma idan famfon ruwan yana kashe kansa ne ta hanyar tabawa ko sansanan wani abu, to ba sai ka yi amfani da wani abu ba. Idan ba haka ba, kana iya amfani da tawul ko gwiwar hannu ko kuma damtsen hannunka wajen rufe famfon.
Busar da hannu
Ka busar da hannunka da tsaftataccen tawul. Koda yake amfani da tawul yana da illa ga muhalli, amma fallen takardar da ake amfani da ita a bayan gida ta fi tawul ko na'urar dumama hannu dacewa a lokacin da aka zo busar da hannu. Sannan idan kana amfani da tawul a gida to ka tabbatar da cewa, kana wanke su daga lokaci zuwa lokaci.