A ranar talata 22 ga watan Yulin shekara ta 2014, na karanta labarin dake karin bayani mai gamsarwa adangane da yadda musulmai a babban masallacin birnin Xining dake lardin Qinghai dake gabashin kasar Sin suke yin azumin watan Ramadan na bana a kasar Sin, lamarin da ya kara tabbatar da cewa, labarin da kafufin yada labaran kasashen Amurka da yammacin suka yayatawa a yan kwanakin nan cewa, ma'aikatun gwamnati a kasar Sin sun hana musulmai yan kabilar Uighur yin azumi da sauran aiyukan ibada a lokacin azumin watan Ramadan, karyace kawai da kokarin bata sunan kasar Sin a idanun duniya. Bisa fahimta ta, gwamnatin kwaminist ta kasar Sin ba sa yin shishshigi ga harkokin aiyukan ibadar musulmai a kasar Sin, kana Sin tana kiyaye martaba da kimar manyan da kananan kabilu da mabiya addinai a kasar Sin. Domun yadda na ga kun nuna photunan musulmai suna shirin yin bude baki a masallaci, ya kara mun fahimtar kasar Sin adangane da yadda kasar Sin ke martaba addinai a kasar Sin. Kazalika kuma, na yi mamaki ganin yadda babban masallacin Donguan dake birnin Xining a lardin Qinghai dake gabashin kasar Sin, fadin masallacin ya kai murabba'in mita 18000 wanda hakan ke alamunta cewa, surutai da babatu da wasu ke yi na bata sunan kasar Sin a duniya, babu gaskiya a labarin da suke yadawa a duniya na muzanta kasar Sin.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.