A ranakun 14 zuwa 15 ga watan Yulin shekara ta 2014, na samu zarafin karanta gudumowar da jagorar shirin kiwon lafiya, malama Tasallah Yuan ta kawo mana dan ilmantar da mu masu sauraro adangane da yadda za mu kula da lafiyarmu yadda yakamata. A hakika dai, wannan saban nazari da malama Tasallah ta kawo mana a shirinta na lafiya uwar jiki, zai taimaka wa milyoyin tsofaffi da ma sauran al'umma adangane yadda tsofaffi masu yawan shekaru a duniya za su kula da lafiyarsu ta hanyar ware jini da motsa jikinsu sosai. Babu shakka, wannan nazari da kwararru a fannin ilmin kiwon lafiya na kwalejin koyarda ilmin kiwan lafiya suka fitar wanda ya nuni cewa, yin tattaki na tsawon mintoci 20 a kowace rana ga tsofaffin da shekarunsu suka wuce 70, amma ba su zarta 90 ba, zai iya taimaka musu wajen ci gaba da yin tafiya ba tare da taimako ba, tare kuma rage musu barazanar samun nakasa, ta yadda har zai kara kyautata zaman rayuwarsu sosai. To, ke nan, ware jini ko motsa jiki yana da taimaka wa tsofaffi wajen kasancewa a cikin koshin lafiya yadda yakamata. Wato, bisa nawa fahimtar, ware jini ko motsa jiki yana da matukar tasiri ga rayuwar tsofaffi bisa la'akari da cewa, masana sun hakankance cewa, motsa jiki ko ware jini ta hanyar tattaki duk da cewar shekarunsu ya riga ya yi nisa ainun. Daga karshe, ina kara yaba wa malama Tasallah bisa kokarinta a koyaushe na kawo mana tsarabar masamman dan kula da lafiyar mutane, masamman ma mu masu sauraron wannan shiri na malama Tasallah a duk mako.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, shugaban club din masu sauraron cri Hausa na Jihar Yobe, Nigeria.




