Tare da fatan baki dayan ma'aikatanku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, ranar Litinin 30 ga watan Satumba na saurari rahotonku na musamman dangane da kaddamar da yankin cinikayya cikin 'yanci (FTZ) na gwaji a birnin Shanghai dake kudancin kasar Sin.
Kodayake, wannan shi ne karon farko da kasar Sin ta kafa irin wannan yankin ciniki mara shamaki a duk fadin kasar inda masana'antu 36 zasu fara cin gajiyar shirin, amma za a iya cewa akwai yakinin samun cikakkiyar nasara bisa manufa musamman idan aka yi la'akari da cewa shirin kafa yankin cinikayyar cikin 'yanci na da nufin kara fadada manufar nan ta bude kofar kasar Sin ga kasashen ketare da kamfanoni na kasa da kasa, kamar yadda ministan kasuwanci na kasar Sin mista Gao Hucheng ya shaida yayin bikin kaddamarwar. Ban da wannan, kuma kowa shaida ne na irin gagarumin tasirin da manufar bude kofa ga kasashen ketare ta yi wajen habaka tattalin arzikin kasar Sin zuwa wani babban mataki cikin shekaru 30 kawai.
Hakika, kafa wannan yanki ciniki mai 'yanci a birnin Shanghai wata kyakkyawar amsa ce ga batun jan kafa da tattalin arzikin kasar Sin ya samu kansa a ciki sakamakon rikicin kudi da dabaibaye kasashen duniya, kana ya samar da wani kyakkyawan yanayin tafiyar da kasuwanci da harkokin masana'antu da ka iya kawo gogayya mai ma'ana sakamakon manufofin tallafawa kasuwanci da harkokin masana'antu da yankin ya tanadar. Ba shakka, batun haraji da sha'anin bincike na jami'an kwastam game da sauran ka'idojin ciniki kan haifar da tarnaki ga harkokin kasuwanci, kuma ga dukkanin alamu kasar Sin ta yi shirin magance wadannan matsaloli wajen shimfida ka'idoji da sauran sharuddan gudanar da hada-hada a wannan yanki na cinikayya mai 'yanci.
A dangane da haka, ina fatan duka manyan kamfanoni da sauran kafofin cinikayya da kasuwanci na duniya za su gabato da bukatarsu ta neaman shiga wannan yanki mai 'yanci na kasar Sin ba ma kawai domin a dama da su ba, a'a har ma don su ci gajiyar alfanun da hakan ke da shi wajen bunkasa tattalin arzikin kasashensu tare da kawo habakar kamfanoni. Na gode.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon-Dabo, Nigeria