Robert Lewis-Lettington, shugaban sashen tsara dokoki na hukumar raya birane ta MDD ya bayyana hakan, yace a mafi yawan kasashen Afrika dokaki ba sa aiki, ya fada a lokacin kaddamar da littafi mai taken muhimmancin tsara dokoki a yankin dake kudu da hamadar saharar Afrika (SSA) a lokacin taron raya birane na MDD wato UN Habitat wanda ke gudana a Nairobi.
Ya bayyana cewa, daga cikin kasashen Afrika 18 da aka yi samfurinsu a shiyyar, birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu ne kadai ya yi cikakken aiwatar da tsarin, yayin da a kasashe mafi yawa tsarin dokokin ba ya aiki.
Lewis Lettington ya ce, ana aiwatar da kashi 85 bisa 100 na dokokin tsara birane ne a helkwatocin mulki na kasashe, yayin da ake aiwatar da kashi 38 bisa 100 na dokokin a sauran birane.
"Hukumar UN-Habitat ta riga ta taimakawa kasashe tare da taimakon gwamnatocin kananan hukumomi da gwamnatin tsakiya na kasashen, " in ji shi. (Ahmad Fagam)