A yau Alhamis din 16 ga wata, an wallafa bayanin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta mai take "Fahimta mai zurfi kan sabon tunanin samun bunkasuwa" a mujallar "Neman Gaskiya" ta kasar Sin.
Bayanin dai ya bayyana cewa, ya kamata a mai da hankali sosai kan aiwatar da tsarin kirkire-kirkire, don sa kaimi ga samun bunkasuwa, kuma kamata ya yi a dora muhimmanci kan aikin kirkire-kirkire, ta yadda za a samu sabon karfin bunkasuwa ta wannan hanya.
Ban da wannan kuma, bayanin ya ce, ya kamata a kafa sabon tsari na bude kofa ga ketare, wanda hakan ke neman a bi tsarin tattalin arzikin duniya bai daya, da nacewa ga tsarin bude kofa ga kasashen waje, da kuma yin amfani da kimiyya ta zamani, da fasahohin gudanar da harkoki da Bil Adama ke kirkirowa.
Haka zalika, kamata ya yi a mai da jama'a a gaban kome a lokacin da ake aiwatar da tunanin samun bunkasuwa, saboda a yanzu har kuma a cikin dogon lokaci mai zuwa, kasar Sin tana cikin matakin farko na tsarin mulkin gurguzu, hakan ya sa tilas Sinawa su yi amfani da sharudda da suke da su, don gudanar da harkoki gwargwadon karfinsu, ta yadda za a yi kokarin cimma burin samun wadata ga duk al'ummar Sinawa. (Amina Xu)