Shugaba Xi ya bayyana hakan ne, yayin taron karawa juna sani game da tsaron al'umma na yini biyu da aka bude a nan birnin Beijing, yana mai cewa ya zama wajibi 'yan sanda su sauke nauyin da JKS da al'ummar kasar suka dora musu a sabon zamani da ake ciki.
Xi Jinping wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya na kasar, ya ce ya zama dole 'yan sanda su kasance masu kwarewar tabbatar da tsaro, ta yadda za su zamo masu kare kyakkyawan tsarin siyasa da zamantakewar al'ummar kasar ta Sin, matakin da zai haifar da cimma nasarorin da aka sanya gaba na kafa kasa mai wadata ga kowa, da cimma muradun karni biyu na kasar, tare da kaiwa ga nasarar farfadowar kasar Sin baki daya. (Saminu)