Makalar ta shugaba Xi na da taken "musaya da koyi da juna tsakanin al'ummu a matsayin muhimmin jigon samar da ci gaba, da wayewar kai ga bil Adama, kuma hanya ta tabbatar da zaman lafiya da ci gaba."
Makalar ta ce akwai bukatar al'ummu daban daban su martaba juna, su kuma rayu cikin aminci, ta yadda musaya da koyi da juna tsakanin su, zai zamo wata gada ta fadada abokantaka tsakanin al'ummun duniya baki daya. Kana hakan ya kasance ginshikin bunkasa rayuwar al'ummu, da hade sassan duniya ta fannin wanzuwar zaman lafiya.
Kaza lika makalar ta yi kira ga fadada tunani tsakanin al'ummu, da kuma bukatar amfani da kwarewa wajen cin gajiyar hakan.
Bugu da kari cikin wannan Makala, shugaban na Sin ya ce Sinawa za su ci gaba da karfafa gwiwar sassa daban daban, wajen aiwatar da manufofin ci gaba ta hanyar kirkire kirkire, don bunkasa rayuwar bil Adama, da al'adu mafiya dacewa, da sa kaimi ga kyawawan manufofi. (Saminu Hassan)