Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana a yau Jumma'a cewa, kasarsa za ta kara yawan ayyukan hidima da kayayyakin da ake shigo da su cikin kasar.
Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da jawabi a bikin bude taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa game da shawarar ziri daya da hanya daya karo na biyu da aka bude a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ya ce, kasar Sin za ta kara rage kudaden harajin da take karba, da kara bude kasuwanninta, tana kuma maraba da kayayyaki masu inganci daga sassan duniya.
Shugaba Xi ya kuma ce, a shirye kasar Sin take, ta kara shigo da kayayyakin amfanin gona, da hidimomi da kayayyakin da aka riga aka sarrafa.(Ibrahim)