A yau ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aikewa takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin sakon ta'aziyya dangane da fashewar iskar gas a rukunin gidajen jama'a a birnin Magnitogorsk dake Rasha.
A sakon nasa shugaba Xi ya ce, ya kadu da samun labarin fashewar, wadda ta haddasa jikkata da hasarar dukiya.
Ya ce, ya yi imanin cewa, karkashin jagorancin shugaba Putin, za a daidaita wannan matsala cikin nasara, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto,
Yanzu haka, an yi nasarar gano gawawwaki 14 bayan aukuwar fashewar. Kana ba a kai ga gano wasu mutane da dama ba, inda ake ci gaba da aikin ceto masu sauran nunfashi sanadiyar hadarin da ya auku a jajiberin sabuwar shekara a birnin mai nisan kilomita 1,400 gabas da birnin Moscow.(Ibrahim)