#BRF2019# Xi Jinping: Sin za ta kara karfin hadin gwiwa da kasa da kasa ta fannin kare 'yancin mallakar fasaha
Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Jumma'a ya bayyana cewa, kasarsa za ta yi kokarin samar da yanayin kasuwa mai kyau dake martaba ilmi da fasahohi, da inganta tsarin dokokin kare 'yancin mallakar fasaha daga dukkan fannoni, a wani mataki na kara karfin hadin gwiwarta da kasa da kasa a fannin kare 'yancin mallakar fasaha. Har wa yau, za ta kara ba da kariya ga 'yancin baki na mallakar fasahohinsu, kuma za ta haramta tilastawa wani ya yi musayar fasahohinsa. Baya ga haka, za ta inganta ayyukan kiyaye sirrin kasuwanci, tare da hukunta ayyuka na keta 'yancin mallakar fasaha. (Lubabatu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku