in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF: Akwai 'yan matan Chibok 100 da har yanzu ba a san inda suke ba
2019-04-22 11:27:38 cri

Kwanan baya, asusun tallafawa kananan yara na MDD wato UNICEF ya ba da wata sanarwa dangane da cika shekaru 5 da mayakan Boko Haram suka sace 'yan mata 276 daga makarantar sakandaren Chibok dake kasar Nijeriya, inda ya ce, ya zuwa yanzu akwai 'yan mata fiye da 100 da ba a san inda suke ba.

UNICEF ya yi nuni da cewa, daga shekarar 2013 zuwa 2017, mayakan sun sace ko kuma tattara kananan yara fiye da 3500 a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, wadanda shekarunsu na haihuwa suka wuce 13 amma ba su kai 18 ba. A shekarar 2018 kawai, an kashe kananan yara 432 ko kuma jikkata su, kana an sace wasu 180, an kuma ci zarafin 'yan mata 43. Don haka, asusun ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya, da ta kara karfin yaki da 'yan ta'adda, ta kuma mai da hankali kan rayuwar kananan yara a wuraren da yake-yake suka shafa, da gaggauta ceto wadanda aka sata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China