in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya da Kamaru na tattauna batun mayar da 'yan gudun hijira 4,000 zuwa gida
2019-04-18 11:01:40 cri

Mahukunta a kasar Kamaru, sun ce shirye shirye sun yi nisa game aikin mayar da wasu daga 'yan gudun hijirar da suka shiga kasar zuwa yankunan su na asali a tarayyar Najeriya.

Gwamnan yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru Midjiyawa Bakari, ya ce nan da ranar 29 ga watan nan na Afirilu, ake sa ran kwashe 'yan gudun hijirar su 4,000 dake zaune a sansanin Minawao na yankin arewa mai nisa a kasar ta Kamaru, bayan da suka amince bisa radin kan su su koma gida.

Mafi yawan 'yan gudun hijirar dai sun fito ne daga yankunan jihohin Borno da Adamawa, to sai dai kuma tsagin 'yan jihar Adamawa ne suka nuna aniyar su ta komawa gida, saboda kyautatuwar yanayin zaman lafiya a jihar su.

Ko da a farkon watan Afirilun nan ma mahukuntan kasar ta Kamaru, sun taimakawa wasu 'yan gudun hijirar su 40,000, cikin jimillar mutane 60,000 da suka tsallaka zuwa cikin kasar komawa gida Najeriya, bayan da suka kauracewa yankunan su na asali gabanin babban zaben kasar na watan Fabarairu.

Rahotannin MDD sun tabbatar da cewa, sansanin Minawao na dauke da 'yan gudun hijira daga Najeriya da yawan su ya kai sama da mutane 57,000 wadanda suka tserewa rikin Boko Haram.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China