in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kwastam ta Kamaru ta kwace magunguna da mai da aka shigar kasar ta barauniyar hanya
2019-04-16 10:15:56 cri

Hukumar kwastam ta kasar Kamaru, ta kwace nau'o'in magunguna da mai, wadanda aka shigar cikin kasar ta barauniyar hanya. Wata sanarwa da aka fitar a jiya Litinin, ta bayyana cewa, an kwace kayayyakin ne a birnin Douala, a wani mataki na dakile kwararar miyagun kayayyaki da magunguna cikin kasar daga kasashen waje.

Hukumar ta kwastam ta ce cikin kayayyakin da aka kwace, hadda kwayoyin tramadol 100,051, da na combiart 100,072, da kuma litar mai 7,000, sakamakon wani aikin hadin gwiwa da hukumar ta yi tare da rundunar sojin ruwan kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, masu simoga na shigar da miyagun kayayyaki daga makwaftan kasashe ta tashar ruwan kasar dake Tiko, sa'an nan su yi amfani da manyan motoci domin dakon su zuwa Douala.

Rundunar 'yan sandan kasar ta ce, kwayar tramadol, na cikin miyagun kwayoyin da aka fi shan su a fadin kasar, inda a yanzu hatta a makarantu ake samun matasa masu mu'amala da kwayar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China