Majalissar gudanarwa ta rikon kwarya ta kasar Sudan, ta sallafi wasu alkalai daga bakin aikin su, a wani bangare na biyan bukatun da masu zanga zanga suka nema, bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar Al-Bashir a makon jiya.
Wata sanarwa da majalissar ta fitar a jiya Talata, ta ambato jagoran majalissar ta soji Abdel-Fattah Al-Burhan, yana bayyana sallamar babban mai shari'a Omer Ahmed Mohamed Abdel-Salam, da mataimakin babban mai gabatar da kara na kasar Husham Osman Ibrahim, da mai gabatar da kara Amer Ibrahim Majid. Kaza lika sanarwar ta bayyana Al-Waleed Sid-Ahmed Mahmoud, a matsayin sabon babban mai shari'ar kasar.
Majalissar gudanarwa ta rikon kwarya wadda sojoji ke jagoranta ce ke jan ragamar kasar Sudan a halin yanzu, ko da yake fararen hula masu bore, na ci gaba da zaman dirshan a sassan kasar, a wani mataki na matsin lambar ganin an mika mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula.(Saminu)