in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sudan ta kudu a Sin ya jinjinawa salon yaki da fatara a Sin
2019-04-16 09:39:46 cri

Jakadan kasar Sudan ta kudu a Sin John Andruga Duku, ya jinjinawa salon yaki da fatara da kasar Sin ke aiwatarwa, yana mai cewa, dabarun da Sin ke bi a wannan fanni, sun kai kasar ga zama ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, wanda hakan darasi ne ga sauran kasashe.

John Andruga Duku, ya ce tsarin musamman na bunkasa tattalin arziki da samar da ci gaba na Sin, zai zame wa kasar sa jagora, a daidai gabar da take yunkurin fita daga yakin basasa na kusan shekaru biyar.

Jakadan wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Sin Xinhua, ya kara da cewa, daya daga dabarun da suka taimakawa Sin yakar talauci cikin shekaru 40 da suka gabata, shi ne bunkasa samar da ababen more rayuwa.

Mr. Duku ya ce, hadin gwiwar kasar sa mai albarkatun mai da kasar Sin, tsari ne na cudanni in cude ka, ya kuma shafi fannonin samar da ababen more rayuwa da kamfanonin Sin ke aiwatarwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China