in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ayyana fadada tallafi ga sashen zirga-zirga na wasu samfuran jiragen sama
2019-04-16 15:55:49 cri

Mahukuntan kasar Sin sun bayyana aniyarsu ta tallafawa zirga-zirgar sumfurin wasu jiragen sama na shiyya shiyya, inda a yanzu samfurin jiragen saman da za su ci gajiyar rangwamen da gwamnati ke samarwa, zai karu daga 7 zuwa 13. Ana sa ran daukar wannan mataki, zai bunkasa hada-hadar sufurin jiragen sama, ya kuma baiwa fasinjoji damar samun karin sauki.

A cewar hukumar dake kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar CAAC, samfurin jiragen sama 13, da suka hada da kirar kasar Sin na ARJ21-700 da MA60, da kuma wadanda ake shigowa da su daga ketare da suka hada da CRJ-900, sun shiga jerin wadanda za su ci gajiya daga wannan manufa.

Bisa wannan tanaji, fasinjojin dake hawa wadannan nau'o'i na jiragen sama, ba za su rika biyan kudaden harajin bunkasa asusun harkar zirga zirgar samaniya ba, wanda gwamnati ke cazar fasinjoji da kamfanonin jiragen sama.

An kiyasta cewa, sabon tsarin zai amfani fasinjoji da yawansu zai kai miliyan 5 a duk shekara, wadanda ke zirga-zirga tsakanin shiyyoyin kasar, inda za su samu ragin da ya kai kudin Sin miliyan 240, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 35.8. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China