in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan za a raya dangantakar dake tsakanin Sudan da Sin zuwa wani sabon matsayi
2019-04-16 13:39:36 cri
A jiya jakadan kasar Sin dake kasar Sudan Ma Xinmin ya gana da shugaban kwamitin soja na wucin gadi na kasar Sudan Abdel-Fattah Al-Burhan.

A yayin ganawar, Ma Xinmin ya bayyana cewa, Sin ta dora muhimmanci sosai ga halin da ake ciki a kasar Sudan, kuma tana fatan za a kwantar da hankali yadda ya kamata a kasar. Sin da Sudan sun sada zumunta a dogon lokaci, da yin imani da juna a fannin siyasa, da raya tattalin ziki da yin ciniki don samun moriyar juna, kana sun fahimce juna da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, don haka su hakikanin abokai ne. Ya ce, Sin tana son ci gaba da tabbatar da raya dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu. Haka kuma, Sin ta yi imani da cewa, Sudan tana da karfi wajen daidaita matsalolinta da kanta da kuma tabbatar da zaman lafiya da na karko a kasar.

A nasa bangare, Al-Burhan ya nuna yabo ga dangantakar abokantaka a tsakanin Sudan da Sin, kana ya nuna godiya ga kasar Sin domin ta nuna goyon baya da samar da gudummawa ga kasarsa a dogon lokaci. Yana kuma fatan za a sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi bisa tushen tabbatar da dangantakarsu a lokacin hukumar wucin gadi a kasar Sudan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China