in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF: Sama da al'ummun yankuna 300 ne suka kauracewa kaciyar mata a Najeriya
2019-02-07 15:54:56 cri
Wani jami'in asusun UNIFEC mai kula da harkokin gaggawa na yara kanana karkashin MDD, ya ce sama da al'ummun yankuna 309 a tarayyar Najeriya sun kauracewa kaciyar mata a shekarar 2018 da ta gabata.

Mohamed Fall, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da aka fitar a Abuja, fadar mulkin Najeriya, inda ya ce sakamakon wani binciken jin ra'ayin jama'a na shekarar 2016 zuwa 2017, ya nuna raguwar aikata kaciyar mata a sassan Najeriya. Mohamed Fall, wanda shi ne wakilin asusun UNICEF a kasar, ya ce sakamakon ya nuna kaso kusan 18.4 bisa dari na mata dake tsakanin shekaru 15 zuwa 49 ne aka yiwa kaciyar a tsakanin wadannan shekaru, sabanin kaso 27 bisa dari da aka samu a shekarar 2011. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China