in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 26 a harin 'yan bindiga a jahar Zamfara
2019-02-06 15:22:38 cri
A jiya Talata 'yan sandan Najeriya sun tabbatar da cewa, mutane 26 aka hallaka kana wasu mutanen 7 aka yi garkuwa da su a wasu jerin hare haren 'yan bindiga biyu a jahar Zamfara dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Maharan dai sun yi dirar mikiya ne kan wasu kauyuka 7 dake gundumar Mada a shiyyar Gusau, babban birnin jahar, da yammacin ranar Litinin, inda suka kashe a kalla mutane 15.

Sai kuma kauyen Batauna shi ma a jahar, inda hukomin 'yan sandan suka ce maharan barayin shanu sun hallaka mutanen kauyen kimanin 11 kana suka cinnawa garin wuta da dare.

Jamia'n tsaro sun gano gawar wata mata daga cikin wadanda aka hallaka a gundumar Mada, sannan sun yi awon gaba da mutum guda da wasu mata 6 inda suka yi garkuwa dasu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China