Mataimakin firaministan kasar Sin zai kai ziyara Amurka don tattauna batun tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu
Kakakin ma'aikatar cinikayyar kasar Sin Gao Feng ya ce, bisa gayyatar da sakataren kudin Amurka Steven Mnuchin, da wakilin kasar mai kula da harkokin cinikayya Robert Lighthizer suka yi masa, mataimakin firaministan kasar Sin Liu He zai kai ziyara Amurka daga ranar 30 zuwa 31 ga wata, don yin shawarwari kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu.
Gao ya bayyana haka ne a gun taron manema labaru da aka shirya a yau Alhamis a nan birnin Beijing. (Bilkisu)