in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta)Ya zama dole kasar Sin ta dinke waje guda in ji shugaba Xi
2019-01-02 16:32:42 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce ya zama wajibi kasar sa ta ci gaba da zama a dunkule, kuma a ci gaba da aiwatar da matakan cimma wannan buri cikin himma da kwazo.

Shugaba Xi wanda kuma shi ne shugaban kwamitin koli na hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar ta Sin, ya bayyana hakan ne a Larabar nan, cikin jawabin da ya gabatar a yayin taron bikin cika shekaru 40 da aikewa da sako ga 'yan uwa mazauna yankin Taiwan.

Xi, ya ce tarihi da sassan doka, sun tabbatar da kasancewar yankin Taiwan wani bangare na kasar Sin, kuma sassa biyu dake hade ta zirin Taiwan, dukkanin su bangarori ne na kasar Sin daya tak a duniya, don haka ba za a taba iya raba su da babban yankin kasar ba.

Shugaba Xi Jinping ya alkawarta aiwatar da "sahihiyar manufa, da aiki tukuru " wajen wanzar da zaman lafiya da dinkewar sassan kasar sa, to amma kuma bai kau da yiwuwar amfani da karfi wajen cimma wannan buri ba. Ya ce wannan mataki bai shafi 'yan uwa dake zaune a yankin Taiwan ba, illa dai sassan kasashen waje dake tsoma baki cikin harkokin kasar Sin, da kuma 'yan tsiraru masu fatan ballewar yankin na Taiwan da ayyukan da suka gudanarwa.

Shugaban na Sin ya ce dinkewar sassan kasar bisa yanayi na zaman lafiya, da akidar kasa daya tsarin mulki biyu, sun yi matukar dacewa da burin da ake da shi, na cimma nasarar dinkewar Sin waje guda.

Daga nan sai ya alkawarta martaba al'adun da zamantakewar al'ummar yankin Taiwan, bisa doro na kare martabar ikon mallakar yankunan Sin, da tsaron kasar, da kishin samar da ci gabanta, tare da tsarin zamantakewar al'ummar kasar baki daya.

Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, al'ummar yankin Taiwan za su kara amfana daga ci gaban kasar Sin baki daya. Ya ce, manufar kasar Sin daya tak a duniya tushe ne na siyasa wajen bunkasa huldar da ke tsakanin babban yankin kasar Sin da kuma yankin Taiwan, kuma huldar za ta kara inganta bisa ga manufar. Kasar Sin daya tak ce a duniya, kuma manufar Sin daya tak a duniya ka'ida ce da kasa da kasa suka amince da ita. Batun Taiwan harkar gida ce ta kasar Sin, wadda bai kamata sauran kasashe su tsoma baki a ciki ba. (Saminu Alhassan, Lubabatu Lei)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China