Hukumar ta NCAC, ta ce ta ware ranar musamman domin nuna wasu daga al'adun kasar Sin masu kayatarwa, ciki hadda rawar dabbar Dragon, wadda daliban sakandare na wasu makarantun Najeriya suka gudanar, domin nuna irin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Najeriya da kasar Sin ta fuskar musayar al'adu.
Da yake tsokaci game da hakan, jami'i mai lura da harkokin raya al'adu a ofishin jakadancin Sin dake Najeriya Li Xuda, ya ce za a ci gaba da bunkasa sha'anin musayar al'adu tsakanin kasashen biyu, matakin da ko shakka ba bu, zai dada inganta hadin gwiwar dake tsakanin su.
Li ya ce ware ranar kasar Sin, a yayin bikin na bana mafarki ne da ya tabbata, ya kuma nuna irin jajircewar mahukuntan Najeriya a fannin bunkasa musayar al'adu da Sin.
Bikin na bana na mako guda, na da taken "sada ayyukan fasahohi da sassaka na Najeriya da sauran duniya". (Saminu)