in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin nune-nunen al'adun yawon shakatawa na Sin a Nijeriya
2018-10-10 10:36:46 cri

An yi bikin nune-nunen al'adun yawon shakatawa na kasar Sin a cibiyar al'adun kasar Sin dake birnin Abuja, fadar mulkin Nijeriya a ranar Litinin da ta gabata. A yayin bikin, masu aikin yawon shakatawa da wasu masana na kasar Nijeriya sun yi shawarwari kan yadda za a inganta hadin gwiwar dake tsakanin matasan kasar Sin da na Nijeriya a fannin yawon shakatawa, ta yadda za a kara sanin al'ummomin kasashen biyu kan al'adun yawon shakatawa.

Mashawarcin jakadan Sin dake Nijeriya kan harkokin al'adu, kana shugaban cibiyar al'adun kasar Sin dake kasar Li Xuda, ya bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan musayar al'adun yawon shakatawa a tsakaninta da Nijeriya, har ma da dukkanin kasashen Afirka, tana kuma fatan samun karin Sinawa dake son kara saninsu game da kasar Nijeriya, da kuma kai ziyara kasar domin yawon shakatawa.

A jawabin da ya gabatar yayin bkin, shugban Kungiyar raya harkokin yawon shakatawa na matasan Nijeriya Okon Emmanuel, ya ce, an yi bikin bayan taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing a watan Satumba da ta gabata ne domin kara musayar al'adu tsakanin matasan kasashen biyu, da kuma raya harkokin yawon shakatawa na kasashen cikin hadin gwiwa.

Wakilai, masana da kuma jami'an da suka zo daga kungiyar raya harkokin yawon shakatawa na matasan kasar Nijeriya, da kamfanin raya harkokin yawon shakatawa, da hukumar gidan talabijin ta Nijeriya, da kuma ofishin UNESCO dake kasar da sauran hukumomin da abin ya shafa ne suka yi shawarwari da wakilan cibiyar al'adun kasar Sin yayin bikin, inda suka kuma amsa wasu tambayoyin 'yan jaridu cikin hadin gwiwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China