Aikin da aka yi masa lakabi da yankin masana'antu mara shinge na kasa da kasa na hadin gwiwar Sin da Uganda, wanda rukunin kamfanin Dongsong Energy zai aiwatar, zai rika samar da gilas da karafa da taki mara sinadaran zamani. Aikin zai kuma samar da guraben aikin yi 3,000 idan aka kammala a shekarar 2020.
Yoweri Museveni ya ce aikin zai rage kudin da ake kashewa na sayo kayayyaki daga waje, wadanda a yanzu za a iya samarwa a kasar.
Ya kuma yabawa kasar Sin bisa kwarin gwiwar zuba jari a Afrika da ta ba kamfanoni masu zaman kansu da na gwamnati.
Shi kuwa Jakadan Sin a Uganda Zheng Zhuqiang, cewa ya yi, aikin shi ne mafi girma da kamfani mai zaman kansa zai yi a Uganda, wanda kuma zai samar da kudin shiga mai yawa. Ya kuma gode da irin goyon bayan da Shugaba Museveni ke ba dangantakar Sin da Uganda. (Fa'iza Mustapha)